Kwankwaso yace ba zai yi magana akan rikicin NNPP ba

0
53

Jagoran jam’iyyar NNPP a matakin kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yace ya yanke hukuncin kin cewa komai akan rikicin siyasar cikin gida da jam’iyyar su ta afka a jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana hakan a yau lokacin da yan jarida suke zantawa da shi a gidan sa dake Miller Road.

Yace bashi da abun fada dangane da rikicin.

Karanta karin wasu labaran:Jam’iyyar NNPP zata ladabtar da gwamnan jihar Kano 

Yace baya son yin magana akan abun da bashi da sha’awar shiga, saboda shugaban jam’iyya na jiha ya rika ya yi magana shikenan.

Idan za’a iya tunawa tun da yammacin jiya litinin aka samu fitar labarin dakatar da sakataren gwamnatin jihar Kano Baffa Bichi, da kwamishinan sifuri, daga NNPP, bisa zargin su da hannu a kafa kungiyar Abba tsaya da Kafarka.

Amman Baffa Bichi yace bashi da hannu a kafa kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here