Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 45 a Kano

0
28
Kano

Shugaban hukumar dakile yaduwar cutuka ta jihar Kano KNCDC Farfesa Muhammad Adam Abbas, yace barkewar cutar amai da gudawa da aka samu kwana kwanan nan a Kano tayi ajalin mutane 45, a kananun hukumoni 28 da cutar ta shiga.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta saka lokacin cigaba da shari’ar masarautar Kano

Farfesa Muhammad, ya sanar da hakan ne a jiya lokacin da yake jawabi a taron bibiyar ayyukan ma’aikatar lafiya da aka shirya a Kaduna.

Yace rashin tsafta, da rashin kula da abinda za’a ci sune manyan hanyoyin kamuwa da cutar, da Kuma yada ta a tsakanin al’umma.

Ya shawarci al’umma dasu zama masu kiyaye tsaftar jiki data abinci musamman tsaftace kayan marmari kafin a kai su baki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here