Gwamnatin Nigeria zata fitar da mutane miliyan 100 daga talauci

0
57

Ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa ta nanata aniyar gwamnatin tarayya da tace tana son fitar da yan Nigeria miliyan 100, daga kangin talauci daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, ce ta kirkiro shirin fitar da yan Nigeria daga talauci ta hanyar samar da sana’o’in dogaro da kai, sai dai a yanzu abin na neman gagara sakamakon yadda yan kasar ke sake fadawa halin talauci da tsadar rayuwa.Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Farfesa Joseph Utsev, a ranar Laraba, ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na magance kalubalen zamantakewa da tattalin arziki.

Karanta karin wasu labaran:Kaso 60 na al’ummar Nigeria suna rayuwa a cikin talauci–Peter Obi

Da yake jawabi a wani taron karawa juna sani a shiyyar Kudu-maso-Kudu kan Kafawa tare da karfafa kungiyoyin masu ruwa da tsaki a harkar noman rani a jihar Akwa Ibom, ministan ya jaddada muhimmancin albarkatun ruwa, yana mai cewa, gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta magance rashin abinci a kasar nan.

Ministan wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Richard Pheelangwah, ya ce gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Bola Tinubu, ta kafa dokar ta-baci kan samar da abinci ta hanyar noman rani.

Ministan ya kara da cewa ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli a wani bangare na alkawuran da ta dauka, ta bayyana bangaren noman rani a matsayin daya daga cikin muhimman manufofin kokarin da gwamnatin tarayya na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here