Majalisar dinkin duniya ta gamsu da kokarin gwamnatin tarayya wajen samar da abinci a Nigeria

0
77

Hukumar bunkasa aikin noma da samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar nan ta yi asarar tan 55,629 na abinci saboda ambaliyar ruwan da aka samu a shekarar 2024.

Kididdigar da hukumar ta fitar ta nuna cewa asarar kayan abinci da aka yi a Najeriya a wannan shekara zata iya ciyar da mutum miliyan takwas da rabi har tsawon watanni shida.

Mataimakin shugaban hukumar a kasar nan, Salisu Mohammed, ya ce sauyin yanayi da hauhawar farashi da matsalar tsaro da kuma lalacewar tattalin arziki, na daga cikin abubuwan da suke kawo cikas ga fannin noman.

Karanta karin wasu labaran:Yan Boko Haram sun yanka manoma a jihar Borno

Bayanin hakan yazo a daidai lokacin da aka gudanar da bikin Ranar Abinci ta Duniya a jiya, wanda bikin ya mayar da hankali wajen yin kira ga gwamnati ta hada hannu da kwararru wajen magance kalubalen karancin abinci mai gina jiki a tsakanin al’umma.

Hukumar ta bayyana gamsuwa da matakan da gwamnati ke dauka wajen wadata kasa da abinci, amma ta yi gargaÉ—in cewa dole sai an kara yin kokari domin samun nasarar hakan.

Idan za’a iya tunawa an samu mummunar ambaliyar ruwa a jihohin kasar nan da dama musamman Jigawa da Borno, wanda baki dayan su sun yi nisa a kokarin samar da abinci mai yawa, amma ambaliyar ruwan ta lalata gonaki da dama.

Wata kididdiga ta nuna cewa jihohin Nigeria mafi yawa sun samu matsalar ambaliyar ruwan a gonaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here