Gwamnatin tarayya ta bayyana masu janyo tsadar abinci a Nigeria

0
74

Hukumar kare hakkin mai siyan kaya ta kasa FCCPC ta zargi masu sayen kayan abinci su na boyewa da cewa sune masu haifar da hauhawar farashin kayan abinci.

Shugaban hukumar, Tunji Bello ne ya bayyana haka ranar Laraba a wani taron masu ruwa da tsaki daya gudana a birnin Kano.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar dinkin duniya ta gamsu da kokarin gwamnatin tarayya wajen samar da abinci a Nigeria

Ya dara da cewa a binciken da hukumar su ta gudanar ta gano yadda wasu ‘yan kasuwa ke rige-rigen saye sabon kayan abinci da aka fara girbewa suna boyewa lamarin da yake kara ta’azzara karancin abincin a kasuwanni, da kuma haifar da karuwar hauhawar farashin kayyakin masarufi.

Tunji, yace mutanen dake aikata wannan mummunan aiki ba su damu da halin da al’ummar Nigeria za su shiga ba, don haka suke zuwa wajen manoma suna sayen kayan abincin da suka noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here