Kotu ta bayar da umarnin gudanar da zaben kananun hukumomi a Kano

0
58

Babbar kotun jihar Kano ta umarci Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano da ta gudanar da zaben kananun hukumomi a gobe asabar 26 ga watan Oktoba.

Kotun ta kuma umarci jami’an  tsaro su shiga zabe da za’a gudanar.

Karanta karin bayani:Hukumar zabe ta jihar Kano ta fara rabon kayan aikin zaben kananun hukumomi

Hukuncin ya sabawa umarnin wata wata kotun tarayya wadda ta rushe shugabancin ma’aikatan KANSIEC, tare da umartar jami’an tsaro karsu halarci wajen zaben har sai an zabi shugabannin da suka cancanta a KANSIEC.

A yammacin jiya alhamis ne rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da cewa jami’anta ba zasu halarci zaben ba saboda yiwa kotu biyayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here