Yan Nigeria miliyan 129 ne suke rayuwa a kuncin talauci

0
123

Farfesa Ahmad Bello Dogarawa, na sashin koyar da aikin akanta dake jami’ar Ahmadu Bello Zaria, yace yan Nigeria miliyan 129 ne suke yin rayuwa a kuncin talauci, wanda sabbin mutane miliyan 29 suka shiga talaucin a cikin shekara guda, kamar yadda wani rahoton bankin duniya ya bayyana a watan Satumba na wannan shekara.

Ya kuma bayyana cewa mabanbancin nau’ukan talauci yakai kaso 63 cikin dari a Nigeria, da kuma karancin kudin shiga a hannun mutane da yakai kaso 40 cikin dari.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron kungiyar Ansar-UD-Deen karo na 9 da aka gudanar a Kaduna, Farfesa Dogarawa ya bayyana cewa, galibin talakawan duniya suna zaune ne a yankin kudu da hamadar Sahara da kuma Kudancin Asiya.

Ya jaddada cewa al’ummar Musulmi, wadanda suka kunshi kashi 54 cikin dari na al’ummar Najeriya, sune ke fuskantar kalubalen talauci musamman a jihohin Arewa.

Dogarawa ya bayyana cewa a tarihi musulmi sun ba da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya amma suna fuskantar kalubalen tattara dukiya da barnatar da tattalin arzikin kasa.

Ya bukaci al’umma da su rika bin halaltattun hanyoyin rayuwa, tare da cewa koyarwar addinin Musulunci na karfafa dogaro da kai da kuma hana zaman banza.

Shugaban kungiyar Ansar-UD-Deen Dr. Abdulrafiu Sanni wanda Alhaji Iskeel Yusuf ya wakilta ya nuna damuwarsa kan yadda al’ummar Musulmi ke fama da matsalolin tattalin arziki tare da yin kira da a dauki kwararan matakai da suka shafi ilimi da kasuwanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here