Gwamnoni da sarakuna suna ganawa a fadar shugaba kasa don nemowa yan kasa saukin rayuwa

0
54

A halin yanzu Gwamnoni da sarakunan Nigeria suna ganawa a fadar shugaba kasa don nemowa yan kasa saukin rayuwa.

Duk da dai ba’a bayyana abubuwan da aka shirya tattaunawa a wajen taron dake wakana a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa ba, amma wata majiya ta ce gwamnonin da sarakuna suna duba hanyoyin da za’a samarwa yan Nigeria saukin masifar tsadar rayuwa da ake ciki saboda cire tallafin man fetur da sauran manufofin gwamnatiin Tinubu ya haifar.

Daily trust, ta rawaito cewa gwamnonin suna son jin ta bakin sarakunan akan yadda za’a fito da hanyar da yan Nigeria zasu samu saukin rayuwa.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kungiyar gwamnonin kasa kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrazak Abdulrahman, sai gwamnonin Delta, Ogun, Oyo, Taraba, Gombe, da Kaduna.

Daga bangaren sarakuna akwai mai alfarma Sarkin Musulmai, da Oni na Ife, sai Etsu Nufi Yahaya Abubakar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here