Gwamnatin tarayya ta biya bashin da ma’aikatan jami’o’i ke bin ta

0
88

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sanar da sakin kudaden da ma’aikatan jami’o’i ke bin ta, na albashin su da aka rike musu.

Ma’aikatan da aka sakarwa kundin sun kasance wadanda ba Malamai ba dake aiki a jami’o’in gwamnatin tarayya, wanda suka hadar da manyan ma’aikatan jami’o’i da kuma ma’aikatan da ba Malamai ba.

Daraktan yada labarai na ofishin babban akanta na tarayya Bawa Mokwa, ne ya tabbatar da sakin kudaden a yau asabar.

Yace an fara da biyan ma’aikatan da ba masu koyarwa ba, wanda tuni wasu sun samu shaidar tura musu kudin.

A ranar litinin data gabata ne kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba Malamai ba suka tsunduna yajin aikin sai baba ta gani saboda rike musu albashin da gwamnatin tarayya tayi na watanni 4.

Yajin aikin ya kawo cikas ga fannin tafiyar da jami’o’in Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here