Ma’aikatan jami’o’in Nigeria sun janye yajin aikin sai baba ta gani

0
93

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba Malamai ba NASU da SSANU, sun sanar da janye yajin aikin sai baba ta gani da suka tsunduna a ranar 27 ga watan Oktoba.

Sun shiga yajin aikin Sakamakon kin biyan su albashin watanni 4 da gwamnatin tarayya tayi.

A yanzu kuwa sun janye yajin aikin saboda tabbacin da suka samu daga bangaren gwamnati cewa an kammala shirin biyan su hakkin da aka rike musu.

Kafin janye yajin aikin sun gana da wakilan gwamnati cikin su harda Ministan Ilimi.

Cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar NASU Prince Peter Adeyemi, ya fitar ya ce shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i Mohammed Ibrahim, ya tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya ta fara biyan kudin albashin da aka rike musu nan gaba kadan.

Kungiyoyin NASU da SSANU, sun umarci daukacin mambobin su shirya komawa bakin aiki daga gobe talata 5 ga wata Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here