A A Rano, AYM Shafa, da Matrix sun yi karar Dangote, akan hana siyo fetur daga kasashen waje

0
76

Dillalan man fetur guda uku da suka hadar da AA Rano, AYM Shafa da Matrix sun nemi kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja, tayi watsi da karar da matatar man fetur ta Dangote ta shigar.

Cikin karar hadin gwiwa da suka shigar a ranar 5 ga Nuwamba, mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/2024, sun ce amincewa bukatar da Dangote ya shigar wa kotu zai kawo koma bayan fannin man fetur a Nigeria.

Inda suke ce bawa Dangote shi kadai damar tafiyar da al’amuran fetur babbar masifa ce ga Nigeria.Tun a ranar 6 ga watan Satumba ne Dangote, ya shigar da hukumar kula da albarkatun Man fetur ta kasa DPR, AYM Shafa, AA Rano, T. Time, da Matrix kara.

Matatar Dangote tana son kotu ta haramta bayar da lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje, kamar yadda dokar fannin fetur ta PIA, ta tanada.

Sai dai wadanda aka shigar da karar sun ce matatar Dangote ba zata iya wadatar da Nigeria da adadin man fetur da take bukata ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here