Gwamnan Kano ya bude asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli

0
92

A kokarin da yake yi na rage yawan mata masu rasuwa lokacin haihuwa, gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bude asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli, bayan gagrumin gyaran da aka yi masa karkashin jagorancin gwamnatin Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yammacin jiya alhamis.

Abba, ya bayyana gamsuwar sa, akan yadda ya duba aikin da aka yiwa asibitin da kuma daga darajar sa, da kayan aiki.

Sannan ya nemi mahukuntan Asibitin su zama basu bayar da kulawar data dace ga sabbin kayan aikin da aka zuba wa asibitin, don samun ingantuwar kula da lafiyar al’ummar Kano.

Haka zalika gwamna Abba, ya tabbatarwa al’ummar cewa gwamnatin sa zata cigaba da bawa fannin tafiya kulawa.

Daga karshe Gwamnan ya jagoranci raba magunguna ga asibitocin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here