Gwamnan Kano zai sauke wasu daga cikin kwamishinonin sa

0
57

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, yace akwai yiwuwar yiwa majalisar zartarwa ta Kano, garambawul, bisa la’akari da kokari ko rashin kokarin kwamishinonin sa.

Abba, ya tabbatar da karbar rahoton dake bayyana irin kokarin da kowanne kwamishina yayi, inda yace nan gaba kadan al’umma zasu ji hukuncin da aka yanke.

Gwamnan, ya sanar da yiwuwar yin garambawul din yayin da yake zantawa da wasu kafafen yada labarai a ranar laraba.

Haka zalika, yace babu wani kwamishina da ya roki a bashi mukamin a baya, inda yace anyi amfani da cancantar kowanne mutum kafin bashi mukamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here