Ganduje yace APC zata dade tana mulkar Nigeria

0
80
Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC dake mulkin Nigeria Abdullahi Umar Ganduje, yace alamu sun bayyana akwai yiwuwar jam’iyyar zata dade tana Mulki a Nigeria, bisa hujjar sa ta cewa APC tana samun farin jini a wajen yan kasar.

Wannan kalamai na Ganduje sun fito cikin wata sanarwar da sakataren yada labaran sa Edwin Olofu, ya fitar a yau Lahadi a Abuja, Sakamakon zaben Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da aka yi.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce sakamakon zaÉ“ukan jihar Edo da kuma na Ondo, alama ce ta cewa ‘yan Najeriya sun rungumi jam’iyyar hannu bibbiyu.

A yau Lahadi ne hukumar zabe INEC ta bayyana Gwamna, Lucky Aiyedatiwa na APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaÉ“en da aka yi jiya Asabar, da Æ™uri’a 366,781, inda zai ci gaba da wa’adinsa na biyu, bayan ya kada babban abokin hamayyarsa Agboola Ajayi na PDP wanda ya samu Æ™uria’a 117,845.

Jam’iyyar PDP ta soki sakamakon zaÉ“en na Ondo da cewa shi ne mafi muni da INEC ta taÉ“a yi.

Babban sakataren yada labaran PDP na kasa Debo Ologunagba ya ce an yi amfani da kuÉ—i wajen sayen kuri’a fiye da hankali, bayan maguÉ—i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here