Yakin cacar baka ya barke tsakanin Obasanjo da fadar Tinubu

0
76

Yakin cacar baka ya barke tsakanin Obasanjo da fadar shugaban Nigeria Tinubu, bayan da tsohon shugaban na Nigeria ya kalubalanci manufofin gwamnatiin Tinubu musamman akan tattalin arziki da walwalar yan kasa.

An jiyo Obasanjo, na zayyano cewa mulkin Tinubu, da tsohon shugaban Nigeria Buhari, sune suka jefa yan Nigeria halin kuncin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

Obasanjo, yace ko kadan manufofin gwamnatiin Tinubu na tattalin arziki basu da wani amfani sai dai kara jefa Nigeria matsalar rashin nutsuwa.

Haka ne yasa wasu daga cikin masu taimakawa Tinubu, mayar da martani ga Obasanjo, inda Sunday Dare, mataimakin shugaban Nigeria Bola Tinubu, a fannin sadarwa da wayar da kan yan kasa, ke cewa Obasanjo ne ya fara lalata Nigeria a lokacin Mulkin sa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Fadar shugaban kasar tace a zamanin mulkin Obasanjo, ya kashe dala biliyan 16, a fannin wutar lantarki amma babu abinda aka samu na cigaban wutar, sai dai barin kasar a cikin duhu kamar yadda APC tace.

Sunday Dare, yace Tinubu yana yin duk abinda zai iya wajen saukakawa mutane kuncin rayuwa.

Amman ana ganin cire tallafin man fetur da Tinubu yayi shine babban abinda ya kara jefa talakawa cikin kunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here