An shigowa da al’ummar Nigeria Sugar mara inganci

0
66

Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki ta Nigeria FCPC, ta bankado wani nau’in sugar mara inganci, wanda ba a yi wa rajista ba kuma ake sayarwa a kasuwannin musamman a jihohin kudu maso yamma da arewa maso gabashin kasar.

FCPC, tace tana yin kokarin magance matsalar bazuwar nau’in wannan sugari, kamar yadda ta bayyana cikin wata sanarwa.

Hukumar, ta kara da cewa wasu mutane ne suke yin satar hanya wajen shigar da sikarin Nigeria daga kasar Brazil.

FCPC, tace sikarin baya dauke da sinadaran da ake bukata masu inganci ga lafiyar dan Adam, wanda hakan ne ya sa wannan sukari yake da hadari ga lafiyar jama’a.

Sikarin kuma ba shi da rajistar hukumar NAFDAC, mai tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta Nigeria.

Hukumar kare hakkin masu sayayyar ta Najeriyar dai ta lashi takobin bin dukkan matakan da suka kamata, wajen ganin ta dakile bazuwar wannan sukari a kasuwannin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here