Cutar Maleriya tana saka Nigeria asarar dala biliyan 1

0
47

Gwamnatin tarayyar Nigeria tace cutar zazzabin cizon sauro tana saka kasar yin asarar dala biliyan 1 da miliyan dari, a kowacce shekara.

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ne ya sanar da hakan lokacin ƙaddamar da taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan yaƙi da cutar a Najeria, wanda aka yi a birnin tarayya Abuja.

Pate, ya ce arziƙin da Nigeria take asara a shekara sakamakon cutar zazzaɓin cizon sauro ya zarta dala biliyan 1.1.

Ministan ya Æ™ara da cewa Najeriya ce ta fi fama da matsalar wannan cuta, inda a shekarar 2022, sama da yara 180,000 ‘yan Æ™asa da shekara biyar suka mutu sanadiyyar cutar, sannan yace za’a iya yin maganin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here