Shugaban Nigeria ya gana da shugaba Macron na Faransa

0
39

Shugaban Ƙasar Nigeria Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci kasar Faransa, a jiya Laraba, wanda a yau alhamis Tinubu, ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron, a fadar sa ta Elysee.

Shugaban yayi ganawar a matsayin ziyarar aiki da yakai tare da tawagar sa data kunshi ministan harkokin waje Yusuf Tuggar da ministan kuÉ—i, Wale Edun da na tsaro Badaru Abubakar.

A É“angare É—aya shugaban Faransa ya shiga É—akin taron tare da Æ™aramin ministan harkokin waje na Æ™asar, Thani Mohamed Soilihi da kuma ministan tsaro na Faransa, Sebastien Lecornu da sauran jami’ain gwamnatin Faransa.

Ana sa ran Najeriya da Faransa za su ƙulla manyan huldar diflomasiyya da kasuwanci a lokacin ziyarar ta shugaba Tinubu, wadda take zuwa bayan ragin samun alkairin da Faransa take samu a Afirka.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da ƙasashen da ta raina a yammacin Afirka, irin su Nijar da Burkin Faso da Mali, musamman akan matsalolin tsaro.

Ƙasashen sun yanke huldar diflomasiyya da kasashen Yammacin turai tare da karkata akalarsu zuwa ɓangaren Rasha.

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, Tinubu ya yi ƙoƙarin ganin ƙasashen Nijar da Mali da Bukina Faso sun koma maamalar dimokuraɗiyya sai dai har yanzu hakan bai yiwu ba.

Sai dai shugaban na Nigeria ya nuna sha’awar sa ta yin tafiya tare da kasar ta Faransa sosai da sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here