Kamfanin yada labarai na Ayrah ya taya Alhassan Yahaya murnar zama shugaban NUJ

0
36

Kamfanin yada labarai, a kafar yanar gizo gizo na Ayrah Media Concept, ya taya Alhassan Yahaya murnar zama sabon shugaban kungiyar yan jarida ta Nigeria wato (NUJ).

Kamfanin Ayrah, dake a matsayin mamallakin jaridar Daily News 24, ya mika sakon murnar bisa nasarar zaben da Alhassan Yahaya, ya samu cikin wata sanarwa da mahukuntan kamfanin suka fitar.

Sanarwar ta yaba da yanayin jagoranci da hangen nesa na Yahaya tare da tsarin kawo sauyi, da bayyana kyakkyawan fata game da jagorantar kungiyar NUJ zuwa ga manyan nasarori a karkashin shugabancin sa.

Sanarwar ta Ayrah, ta Kuma bayyana farin ciki da cewa kwarewar da sabon shugaban yake da ita a fannin aikin jarida zai kai ga samar da cigaban da ake bukata a kungiyar NUJ.

Ayrah Media Concept, sun yaba da sadaukarwar Yahaya, a fannin haÉ“aka Æ™wararrun yan jarida da riÆ™on amana a aikin jarida, yayin da yake kokarin magance matsalolin da ke tasowa a cikin masana’antar yada labarai.

Sanarwar ta kara da cewa, Mun yi imanin cewa a karkashin jagorancinsa, NUJ za ta ci gaba da kare muradun ‘yan jarida tare da daukaka matsayin sana’ar a fadin Najeriya.

Ayrah Media Concept ta sake jaddada goyon bayanta ga shugabancin Yahaya, kuma ta yi alkawarin hada kai da kungiyar NUJ domin karfafa aikin jarida da inganta harkar yada labarai a Najeriya.

Haka zalika sanarwar tace Ayrah, na fatan yin aiki kafada da kafada da NUJ karkashin jagorancin Yahaya, don ci gaba da manufofin da za su amfanar da al’ummar dake yin aikin jarida

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here