Kungiyar kwadago za ta tafi yajin aiki saboda karancin mai da kash

0
80

Kungiyar kwadago a Najeriya ta yi barazzanar tafiya yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, sakamakon karancin kudi da tsadar man fetur da suka addabi kasar.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan zaman tattaunawar da kungiyar ta gudanar kan halin da ma’aikata ke ciki saboda tsadar mai da kuma karancin kudi.

Ya ce kungiyar za ta gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, idan har gwamnati ta gaza magance matsalar karancin kudi da kuma wadata ‘yan kasar da man fetur, daga nan zuwa wa’adin da suka dibar mata.

Sauya wasu daga cikin takardun Naira da sunan hana amfani da tsoffin takardun kudin da babban bankin kasar CBN ya yi, ya jefa al’ummar Najeriya cikin mawuyacin hali, abin da ya haifar da zanga-zanga musamman a kudancin kasar.

Zanga-zangar a wasu yankunan dai ta haifar da kona bankuna, sakamakon dogon layin da ake samu, ba tare da jama’a sun samu biyan bukata ba.

Haka zalika tsadar man ta jefa mutane da kuma ‘yan kasuwa cikin yanayi maras dadi, inda ‘yan kasar ke koka wa tare da kiraye-kirayen ya kamata gwamnati ta sassauta musu.

Kungiyar NLC dai ta ce, karancin mai da tsadar sa ya yi kamari a kasar, don matsawar gwamnatin Najeriya ta gaza shawo kan wannan matsala, to kuwa ba ta da zabi face tafiya yajin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here