AC Milan ta karbi bakuncin Napoli a Champions League wasan farko zangon Quarter finals ranar Laraba.
Sai dai Napoli za ta buga wasan ba tare da Victor Osimhen ba, wanda ke jinya, na daya a ci wa kungiyar kwallaye a kakar nan.
Dan wasan Najeriya ya dora Napoli a gurbin lashe Serie A na bana a karon farko bayan 1990, mai kwallo 21 a babbar gasar tamaula ta Italiya.
Mai tsaron bayan AC Milan Theo Hernandez ya ce ”Ba wani sauyi da za a samu don Osihmen bai buga karawar ba, Napoli suna da kwarrarrun ‘yan kwallo da yawa”
Kungiyoyin sun kara a bana a Serie A:
Serie A Lahadi 2 ga watan Afirilun 2023
- Napoli 0 – 4 Milan
Serie A Lahadi 18 ga watan Satumbar 2022
- Milan 1 – 2 Napoli
Napoli tana matakin farko da tazarar maki 16 tsakaninta da ta biyu, AC Milan tana ta hudu a teburin Serie A na ban da tazarar maki 22 tsakaninta da Napoli.
Napoli ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da Eintracht Frankfurt, ita kuwa Milan Tottenham ta cire daga gasar ta zakarun Turai.
Daga daga fitattun ‘yan wasan Milan, Khvicha Kvaratskhelia zai iya taka rawar gani, bayan da Osimhen ba zai buga karawar ta hamayya ba.
Wata tara baya ba a san da sunan dan kwallon ba, bayan da Kvaratskhelia ya taka leda a gasar Georgian da ta Rasha da karawa biyu a Europa Conference League.
Yanzu dan kwallon Gerogia ya zama fitatce kuma daya da yake taka rawar gani a Serie A tare da Napoli, wadda ke daf da daukar kofin Italiya na kakar man.
A gasar Serie A ya ci kwallo 12 ‘yan wasa hudu ne a gabansa, ya bayar da kwallo 10 aka zura a raga, shine kan gaba a wannan bajintar.
Dan kwallon Paris St-Germain, Lionel Messi da Neymar da na Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani da na Arsenal Bukayo Saka sune suka ci kwallo sama da 10 da bayar da sama da 10 aka zura a raga a manyan gasar Turai biyar.
A Champions League ba wanda ya kai Kvaratskhelia, wanda ya bayar da kwallo hudu aka zura a raga a gasar.
Saboda haka wasan zai zama mai zafi kuma na hamayya da za a kece raini tsakanin manyan kungiyoyin Italiya.