Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso birnin tarayya Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki takwas a kasar Saudiyya, inda kuma ya gudanar da Umrah.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, yace, jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 5:08 na yamma, bayan daukar kusan sa’o’i bakwai maimakon sa’o’i hudu zuwa biyar daga Jeddah zuwa Abuja, an samu tsaikon ne sakamakon halin da ake ciki a kasar Sudan, wanda matakan tsaro suka hana tashi da sauka ko kuma ratsa duk sararin samaniyar kasar don kaucewa tayar da wani rikici.
Jirgin shugaba Buhari ya taso ne daga Jeddah na kasar Saudiyya inda ya ratsa kasashen Eritrea, Habasha, Kenya, Uganda, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kamaru sanna ya sauka gida Nijeriya.
Bayan ya isa Abuja lafiya, shugaban ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari da mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda Danmallam Mohammed, wanda ya wakilci babban sufeton ‘yan sanda da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Yusuf Magaji Bichi a filin jirgin.