A ranar Talatar da ta wuce ne gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da masana’antar sarrafa zinare a Jihar Kogi da ke arewacin kasar.
A yayin kaddamar da wajen a Mopa mai nisan kilomita 300 da ga Abuja, babban birnin Nijeriya, Ministan Albarkatun Kasa da Tama da Karafa Olamilekan Adegbite ya ce kaddamar da masana’antar a yanzu za ta kawo karshen wahalhalun da masu sana’ar zinare ke fuskanta a yankin.
Nijeriya kasa ce da Allah Ya albarkace ta da ma’adanan karkashin kasa da dama da suka hada da danyen man fetur da tama da karafa da zinare da sauran su.
Tsawon shekaru kasar ba ta amfana kai tsaye da mafi yawan wadannan albarkatun ba, inda ta fi karkata ga man fetur kawai wanda ya zama babbar hanyar samun kudin shiga ga Nijeriya.
Zinare na daya daga kayayyakin da suke da daraja a ko ina a duniya. Hakan ya sanya duk kasar da take da arzikin sa to ba karamar albarka ta dace da ita ba.
A Nijeriya akwai yankunan da bincike ya tabbatar suna dauke da arzikin zinare a karkashin kasarsu, musamman a jihohin Kogi da Zamfara.
A wasu yankunan na arewacin Jihar Kano ma ana hakar zinare amma ba bisa ka’ida ba.
Gwamnati ta yi abun a-zo-a-gani
Tuni masu sharhi suka fara bayyana alfanun da wannan masana’anta za ta yi ga ci gaban yankin da ma kasar baki daya.
Alhaji Ibrahim Wudilawa wani kwararren mai hakar ma’adanai ne a Jihar Kano da ke arewa maso-yammacin Nijeriya, kuma a tattaunawarsa da sashen Hausa na TRT Afirka, ya bayyana irin jin dadinsa game da wannan cibiya da gwamnatin Nijeriya ta kafa.
Ya ce “Kafa wannan cibiya abu ne na farin ciki domin yana daga matakan farko da gwamnati ta dauka don inganta ayyukan haka da sarrafawa da sayar da zinare a kasuwar duniya.”
Minista Adegbite ma ya kara da cewa kafa cibiyar zai kawo karshen amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen haka da kasuwancin zinare a kasar.
“Zabar Mopa a matsayin wajen da za a kafa cibiyar sarrafa zinare ya zo ne saboda hasashen da aka yi na cewa yankin shi ne ya fi yawan albarkatun zinare a Nijeriya.
“A saboda haka masu kasuwancin zinare da ke jihohin Schist Belt masu arzikin zinare za su iya zuwa masana’antar don a sarrafa musu zinarensu ba tare da shan wata wahala ba,” in ji minister Adegbite.
Haka zalika Adegbiye ya kara da cewa wannan muhimmin mataki ya kawo karshen fadan kan iyaka da ake yawan samu tsakanin jihohi.
Amfani biyar da bude wannan cibiya ke da shi ga Nijeriya
1. Samar da ayyukan yi
Minista Adegbite na Nijeriya ya ce kafa cibiyar zai bude kofar samar da sabbin ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya, habaka fitar da ma’adanai da jan ra’ayin masu zuba jari.
Sabuwar cibiyar sarrafa zinaren za ta zama wata babbar sila ta samar da ayyukan yi ga matasana yankin da ma wasu garuruwa, duba da yadda masu sana’ar hakar zinare za su dinga kaiwa da komowa zuwa yankin, za a samu tagomashi sosai.
2. Bunkasa tattalin arziki
Za a iya cewar kaso mafi tsoka na kudin shigar Nijeriya ya dogara ne kan albarkatun man fetur.
Wudilawa ya ce “Duk da cewar akwai ma’adanan kasa da dama a kasar, amma ba a iya samun damar fito da su ba ko ba su muhimmancin da aka bai wa man fetur.
“A yanzu da aka fara kafa cibiyar sarrafa zinare, tattalin arzikin kasar zai samu karin kudade daga wannan bangare,” in ji shi.
3. Saukakawa masu hakar ma’adanai wankewa da sarrafa zinare
Duk da kasancewar kafin a samar da wannan cibiya ana hakar arzikin zinare, amma kuma sai dai masu hakar kan fita da shi zuwa kasashen waje ne a sarrafa musu a can.
“A yanzu ga shi an samar da wajen sarrafawa a gida, wannan zai saukaka musu tare da hanzarta amfana da jin dadin arzikin da suke hakowa, domin za a hako shi a Nijeriya a kuma sarrafa shi a cikin kasar,” in ji Wudilawa.
4. Za a nayar da hankali kan wasu albarkatun kasa baya ga man fetur
A Nijeriyar da aka mayar da hankali kacokan kan albarkatun mai, a yanzu kuma da wannan ci gaba, ana ganin hankula za su fara karkata ga albarkatun kasa irin su zinare.
Masu sharhi na ganin yadda aka fara kafa cibiyoyin sarrafa irin wadannan ma’adanai masu daraja, za a mayar da hankali sosai wajen shiga kasuwancin zinare a kasar.
Ba mamaki nan da wani lokaci a samu bude karin wasu cibiyoyin na sarrafa zinare a Nijeriya musamman a wasu yankunan da suke da shi a karkashin kasa.
Ibrahim Wudilawa ya kuma kara da cewa “Idan hukumomi suka shiga tare da samar da tsari mai kyau, to lallai za a samu masu zuba jari masu zaman kansu a wannan bangare wanda hakan ba karamin ci gaba zai kawo wa ayyukan hakar ma’adanai da sarrafa su a Nijeriya ba.”
4. Daga martabar Nijeriya a idon duniya
Masu ayyukan hakar ma’adanai da kasuwancinsu irin su Ibrahim Wudilawa na kallon kafa cibiyar sarrafa zinare ta Mopa da wani muhimmin mataki da zai daga mattabar Nijeriya a idon duniya.
Wudilawa ya ce, idan har aka dauki matakan da suka kamata, to ba daga cikin Nijeriya kadai ba, har ma daga kasashe makota za a iya kawo zinare a sarrafa shi tare da yin kasuwancinsa a kasar.
“Nijeriya na iya zama wata cibiyar kasuwancin zinare ta Afirka.”
5. Bin sahun manyan kasashen duniya
Alhaji Ibrahim Wudilawa ya yi kira ga mahukunta da su bi sahun sauran manyan kasashen duniya da ke da matattarar zinare wato ‘Gold reserve’ a Turance, inda za a dinga tattara arzikin zinare a wajen.
Kuma wannan cibiya da aka kafa na iya zama babban samar da wannan waje mai matukar muhimmanci.
Ya ce “Muna kira ga gwamnati, baya ga cibiyar sarrafa zinare, akwai wani ma’adani da ake kira ‘Bryte’ wanda ake amfani da shi wajen hakar albarkatun mai.
“Akwai shi da yawa ana fito da shi amma a Nijeriya amma ba a sarrafa shi. Idan za a samar da injina da kayan aikin sarrafa shi a nan, to hakan zai amfanar sosai.”
Wudilawa ya nemi gwamnati da ta tallafa wa masu sha’awar kawo irin wadannan injina da za su dinga sarrafa ma’adanai ta yadda hakan zai amfani Nijeriya da jama’arta. Haka zai sanya a bunkasa kasuwannin kasar a kudu da arewa.
Ya kuma ce “Ba wai gwamnati ta bai wa mutane kudi kyauta ba, a sayo injina a raba wa mutane, a ba su a cikin sauki na wani dan lokaci, gwamnati ta dinga sanya idanu tana tabbatar da lafiyarsu. Hakan zai sanya a samu ayyukan yi a rage dogaro da gwamnati.”
Hasashen da masana suka yi ya bayyana adadin zinaren da aka samu a Nijeriya a 2020 ya kai yawan kilogram 1,520.