Raunin na Camavinga dai babban kalubale ne ga tawagar Carlo Ancelotti da ke fatan kai wa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai idan har ta iya nasara a haduwar ta gobe tsakaninta da Manchester City, wadda a haduwar farko suka tashi wasa kunnen doki wato daya da daya.
Camavinga dai ya taka muhimmiyar rawa a canjaras din Madrid da City makon jiya, haka zalika anga rawar da ya taka a nasarar bara da Madrid din ta fitar da City daga gasar dalilin da ya sa ake kallon tasirinsa a cikin tawagar ta Ancelotti yayin wasan na gobe.
Duk da cewa ana ganin Camavinga a sahun wadanda suka tafka kuskuren da ya bai wa Kevin De Bryune damar farko kwallon da Vinicius ya zura a makon jiya amma lura gurbin da ya ke rikewa a cikin tawagar Ancelotti ka iya haduwa da matsala a wasan na gobe.
Madrid wadda ke rike da kambun gasar na zakarun Turai na neman yin dukkan mai yiwuwa don kare kambunta yayinda Manchester City ke ci gaba da kishirwar kofin wanda har zuwa yanzu ta gaza kai wa gida duk kuwa da tsabar kudin da ta zuba wajen sayen manyan ‘yan wasa da kuma kawo shi Pep Guardiola.