Yadda kayan masarufi ke tashin gwauron zabi a Najeriya

1
169

Yan Najeriya sun damu da halin da suka tsinci kansu na ci gaba da fuskantar hauhawan farashin kayan abinci. 

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci daga shekara zuwa shekara na kara ta’azzara.

A cewar NBS, hauhawar farashin kayan abinci, ya karu da kashi 22.22 a cikin dari a cikin watan Afirilun 2023.

A baya farashin kwandon tumaturi ya kai daga Naira 90,000 zuwa Naira 100,000, sabanin yadda a baya ake sayar da kwandon sa daya akan Naira 20,000.

Har ila yau, farashin kwandon tattasai wanda a baya ake sayarwa akan Naira 12,000 zuwa Naira 15,000, a yanzu ana sayar da shi Naira 40,000 zuwa Naira 45,000.

Sauran kayan abincin kamar su taliyar leda mai dauke da guda 20 duk katan daya ana sayar da ita kan Naira 10,200.

Haka taliyar ‘yan yara mak dauke da guda 40 a cikin leda, ana sayar da duk katan daya kan Naira 8,000.

Baya ga hauhawar farashin kayan abincin da ake ci gaba da fuskanta, an kuma danganta tashin gwaron zabin kayan abincin akan tsadar farashin man fetur da faduwar darajar Naira da kuma karancin kayan aikin gona.

Wadannan matsalolin da aka zayyano, kari da kalubalen rashin tsaro a kasar nan sun kara jefa musamman talakawan kasar nan a cikin halin kuncin rayuwa.

A daya bangaren, wasu daga cikin manoman kasar nan, na ci gaba da fuskantar tsadar farashin kayan aikin noma, musamman saboda tsadar farashin takin zamani da magungunan kashe kwari da rashin samun ingantaccen irin noma da kuma rashin samar masu da kyayawan tsari, don yin noman rani.

Wani magidanci dan shekara 47 mai suna Emmanuel Ikechukwu da ke zaune a yankin Orozo da ke Abuja, wanda kuma yake da iyalai shida, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya taba fuskantar matsin ruyuwa da ta hade masa da hauhawar farashin kayan abinci da tsadar sufuri.

Wasu magidantan na ta hakilon samar wa iyalansu abin da za su ci, amma farashin kayan abincin, sai kara hauhawa yake yi.

Wasu gidajen da dama sun rage yawan kayan abincin da suke sayawa ahalinsu, haka sun dakatar da sayen manya kayan more rayuwa da suka saba siya.

Wani malamin makaranta mai suna Mallam Abubakar Usman, wanda ke zaune a yankin Karu a Abuja, shi ma kokawa ya yi akan hauhawan farashin kayan abincin.

Abubakar, ya ce “A yanzu haka ni da dan uwana, muna tsallake cin abinci har da ‘ya’yana uku saboda tashin gwaron zabin na kayan masarufin.”

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here