Tallafin mai: Tinubu ya nemi sahalewar majalisa don samar da kudaden rage radadi ga talakawa

0
152

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rubutawa majalisar wakilai wasika kan neman gyara a kwarya-kwartar kasafin kudin shekarar 2022 don samun amincewar daukar Naira biliyan 500 domin ‘Yan Najeriya da nufin rage radadin janye tallafin man Fetur.

A ranar Laraba, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta wasikar shugaba Tinubun a zauren majalisar.

Abbas ya ce bukatar ta zama dole domin baiwa gwamnati damar ragewa ‘yan Nijeriya radadin cire tallafin man fetur.

“Na rubuta wasika don neman a yi wa dokar karin kasafin kudin 2022 kwaskwarima. Bukatar ta hakan ta zama dole don samar da kudade da abubuwan da suka dace don rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.

“Don haka, muna bukatar ciro Naira biliyan 500 daga cikin karin kasafin kudin shekarar 2022 na Naira biliyan 819, 536, 937, 937, 803 don samar da kayan tallafi ga ‘yan Nijeriya sakamakon cire tallafin fetur,” in ji wasikar.

Ya bukaci majalisar cikin ​​“gaggauta” da ta yi la’akari da bukatar hakan don baiwa gwamnatinsa damar samar da abubuwan jin kai ga ‘yan Nijeriya.

Bayan karanta wannan wasika, kakakin ya ce, majalisar za ta fara nazarin bukatar shugaban a zauren majalisar ranar Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here