Shinkafar da muka kama ba ta tallafi bace—-Muhyi Magaji

1
41

Hukumar karbar koke koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC ta janye kalamanta akan zargin karkatar da shinkafar tallafin Kano har buhu 16,800, da tayi zargin an sauyawa mazubi domin siyarwa.

Da farko an jiyo shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa wasu mutane ne suka tsegunta musu wani runbun adana kayayyaki da ake sauya mazubin shinkafar tallafin buhu 16,800 da gwamnatin tarayya ta bayar don rabawa a Kano, wanda aka ce wasu mutane sun karkatar da ita tare da sauya mata mazubi don kaiwa kasuwa.

Sai dai a yau lokacin gudanar da taron manema labarai, Muhyi Magaji Rimin Gado, yace binciken farko da suka yi ya nuna cewa shinkafar an shigo da ita jihar Kano daga jihohin Bauchi da Zamfara.

Amman a ranar talata data gabata anga shinkafar dauke da hoton shugaban kasa Tinubu, tare da rubutun cewa tallafin azumin Ramadan ce, kuma ba ta siyarwa bace da aka bankado a wani wajen adana kayayyaki a unguwar Hotoro.

Wakilin jaridar Daily trust, yace yana wajen lokacin da suka tarar ana sauyawa shinkafar mazubi daga buhu mai dauke da hoton shugaban kasa Tinubu, zuwa buhun shinkafa na yan kasuwa, amma du da haka Muhyi Magaji Rimin Gado, yace binciken da suka yi bayan bankado shinkafar ya nuna musu cewa ba ta tallafi bace ta kasance mallakin wani babban dan kasuwar da ba’a bayyana sunan sa ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here