Gwamnatin Nigeria ta bawa kamfanin Process Design and Development Limited, damar samar da matatar man fetur a jihar Gombe, dake daya daga cikin jihohin arewacin kasar.
Mahukunta a fannin na fetur sun bayar da lasisi ga kamfanin don samar da matatar a yankin Dole-Wure, dake karamar hukumar Akko ta Gombe.
Sanarwar hakan ta fito cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur ta kasa NMDPRA ta fitar a shafinta na X ranar Alhamis.
Ana sa ran bayan kammala matatar za ta riƙa tace ganga 27,000 ta danyen man a kowace rana.
Process Design and Development Limited kamfani ne na Najeriya wanda aka assasa a Jihar Kano, kuma anyi
masa rijista tun a watan Agustan 2003.
A watan Oktoban shekarar 2019 ne Kamfanin Mai na (NNPC) ya sanar da gano É—anyen man fetur a Kolmani mai iyaka da jihohin Bauchi, Gombe da Yobe.
NNPC ya ce adadin man da aka gano a yankin ya kai yawan da za a iya yin cinikayyarsa.
Sannan ana ganin hakan zai janyo hankalin masu zuba jari daga ƙetare da kuma bunƙasa tattalin arziki da samar da aikin yi.
A watan Nuwamban 2022 ne tsohon Shugaban kasa Buhari ya ƙaddamar da aikin fara tonon rijiyoyin mai a yankin da ya haɗa da Jihar Bauchi da Gombe da Yobe da Adamawa.
Idan haka ya tabbata wannan shine karon farko da za’a fara hako man fetur a arewa, wanda aka sanar da cewa akwai karin wasu jihohin masu arzikin fetur a arewa amma ba’a yin wani kokarin hako shi.