Oando ya siyarwa da NNPC gidajen mai 380 

0
82

Kamfanin mai na NNPC ya saye kamfanin mai na Oando da cibiyoyinsa 380 da suka hada da gidajen man fetur da iskar gas da man jirgin sama da ke Najeriya da kasar Togo.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce sayen karin gidajen man tare da rumbunan ajiyar mai da tashoshin sarrafa man injina 380 da suka yi, baya ga gidaje 550 da NNPC ke da su, wani yunkuri ne na mayar da NNPC kamfanin mai mafi girma a Afirka.

Da yake jawabi a taron kaddamar da kadarorin Oando da suka koma ma NNPCL a Abuja, Kyari ya ce, “Sayen karin cibiyoyin mai 380 da muka yi na daga cikin shirinmu na ganin NNPCL ya mallaki cibiyoyin mai 1,500 nan ba da jimawa ba, domin ya zama kamfanin mai da babu kamarsa a fadin Afirka.

Ya ce an dauki matakin ne domin fadada bangaren kasuwancin man NNPCL da nufin ingantawa da samar da wadataccen makamashi da kuma samun riba a bangaren a Najeriya.

“Bayan kammala sayen kadarorin Oando, yanzu NNPC na da wurin ajiye jirgin ruwa mai daukar metric ton 240,000 a wata, tashoshin iskar gas takwas, masana’antar sarrafa man inji takwas, gidajen man jirgin sama uku da kuma rumbunan ajiya gida 12,” in ji Kyari.

Ya yi jinjina ga Kwamitin Amintattu na NNPCL bisa sayen Oando da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne Ministan Albarkatun Mai, bisa matakan da ya dauka na bunkasa bangaren domin samar da isasshen mai. 

Kyari ya ce kamfanin na kulla kasancen kasuwanci domin samun nasara, yana mai bai wa ’yan Najeriya tabbacin samun riba a kamfanin.

 

AMINIYA