Gwamnatin Italiya ta mikawa Jamhuriyuar Nijar jiragen saman yaki masu saukar ungulu guda 2 domin yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar.
Ministan tsaron kasar Lorenzo Guerini ne, ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Bazoum Mohammed a fadarsa dake birnin Yammai, domin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Lorenzo yace a karkashin yarjejeniyar hadin kan dake tsakanin kasashen, kasar Italia ranar Talata ta mikawa Nijar jiragen guda 2, yayin da a shekara mai zuwa zata sake gabatarwa kasar da wasu jiragen guda 2.
Ministan yace wannan kadan ne daga cikin romon dangantakar dake tsakanin su, domin kuwa kasashen zasu ci gaba da aiki tare domin cimma muradunsu.
Lorenzo ya bayyana gamsuwarsa da yadda dangantakar kasashen ke tafiya da kuma irin nasarorin da suka samu a bangaren sojinsu wadanda ke gudanar da aikin su da kwarewar da ake bukata.
Ministan yace ziyarar ta Nijar ta bashi damar nazarin hadin kan sojin dake tsakanin kasashen biyu da kuma nasarar da aka samu.