Cristiano Ronaldo ya zama mutum na farko da ya ci kwallo a gasar cin kofin duniya sau biyar a ranar Alhamis bayan da ya zura kwallon farko a bugun fenariti a wasan da Portugal ta doke Ghana da ci 3-2.
Ronaldo ya shafe tarihin da Pele da Uwe Seeler na kasar Jamus da Miroslav Klose, suka kafa a gasar cin kofin duniya.
A makon nan ne Manchester United ta ta raba gari da Ronaldo bayan ya soki kungiyar da kocinta Erik ten Hag a wata hira da yayi da gidan Talabijin.
Hankula dai ya karkata kan Ronaldo, kan ko zai iya kafa wannan tarihi, kuma dan wasan ya samu damar hakan cikin minti na goma da take wasa, to sai dai alkalin wasa ya soke kwallon, amma daga bisani ya samu wannan dama a bugun daga kai sai mai tsaro gida.
Ronaldo dai ana masa kallon babbar barazana ga sauran kasashen da ke rukuni guda da Portugal.