Lionel Messi ya kama hanyar cimma burinsa na lashe gasar kofin duniya, bayan da ya taimakawa kasarsa Argentina doke Croatia da ci 3-0 a zagayen kusa da na karshe da suka fafata daren Talata, inda suka wuce wasan karshe na gasar.
Croatia ta nuna bajinta wajen korar Brazil a wasan zagayen daf da na kusa da na karshe da suka kara, amma sun fuskanci turjiya a filin wasa na Lusail, yayin da Argentina ta ci gaba da rike tarihin rashin doke ta a zagayen kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya.
Messi ne ya bude wa Argentina kofar cin kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ya zama dan wasan tawagar kasar da yafi kowa cin kwallo da kwallaye 11.
Julian Alvarez ne ya zura sauran kwallaye biyu da Argentina ta yi galaba kan Croatia.
Sau biyu Argentina ke lashe gasar cin kofin duniya a tarihinta wato 1978 da 1986.
Tarihi
Lionel Messi ya kafa tarihin lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi nuna bajinta a wasannin na FIFA karo na 10 a gasar cin kofin duniya, a wasan da Argentina ta doke Croatia ci 3 – 0.
Messi ya kuma kafa tarihin lashe kyautar dan wasan da ya fi nuna bajinta a wasannin siri daya kwalle MOTM na gasar cin kofin duniyar na wannan shekara a Qatar.
Kyautar da dan wasan mai shekaru 35Â ya mallakawa abokin taka ledarsa Julian Alvarez da ya ci kwallaye biyu a wasan bayan zakulo finaratin da Messi ya zura kwallo.