An fara shirye-shiryen mayar da dakin otal din da Lionel Messi, ya zauna lokacin da aka yi Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar wajen tarihi.
Messi dai ya jagoranci Argentina wajen lashe kofin duniya, bayan da ta lashe gasar 1986, bayan doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Messi mai shekaru 35 ya lashe gasar a karon farko a tarihin rayuwarsa.
Dan wasan dai a iya cewa ya zama gagara badau, inda ya lashe kusan kowace gasa da ya taba bugawa a rayuwarsa.
Dakin dai za a mayar da shi wajen tarihi idan magoya baya za su koma kallon wajen da zakaran na duniya ya dinga kwana.