Asalin abin da ya faru tsakanin Abba Gida-gida da Aisha Bichi

0
131

A makon jiya ne aka samu wata takaddama a tsakanin dan takarar gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida da Uwargidar shugaban Hukumar DSS Aisha Yusuf Bichi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a yayin da magoya bayan mutanen biyu suka tayar da jijiyar wuya a tsakanin su har ta kai ga furuce-furuce a kafafen sadarwa na zamani, Wakilanmu sun bi diddigi don gano asalin abin da ya faru da kuma yadda abin ya nemi ya tunbatsa har ya kusan daukar sabon salo.

Matar babban daraktan tsaro na farin Kaya na kasa (DSS) ta sa an tsare dan takarar kujerar Gwamnan Kano na Jam’iyyar NNPP na Kano Injiniya Abba Kabir Yusif Wanda a kafi sani da (Abba Gida-gida) tare da bada umarnin lakadawa hadiminsa duka a filin sauka da tashin jirgen sama a Malam Aminu Kano.

Kamar yadda rahotanni suka nuna mai dakin babban Darakta hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Aisha Yusuf Bichi, ta bada umarnin a tsare dan takarar Gwamnan na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta hana shi hawa jirgi da ga Kano zuwa Abuja.

Dambarwar ta faru ne a kofar shiga bangaren matafiya masu ido da Kwalli (alfarma) na filin sauka da tashin jirgen sama na Malam Aminu Kano, yayin da ayarin motocin Abba Kabir Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-gida, su ka haifar da cinkoso a lokacin da ita uwargidan Gidan babban Daraktan Hukumar tsaron farin kayan ke Kan hanyarta ta shiga filin Jirgin.

Lamarin da ya haifar wa da ayarin motocin da ke tare a taron Aisha Bichi tsaiko, yayin da ta ke shiga bangaren masu ido da kwallin domin tashi zuwa Abuja.

Wannan cunkoso da motocin wancan dan takara ya haifar ne ya fusata Aisha Bichi, inda dogarawanta su ka rika duka kan mai uwa da wabi da ababen hawa saboda raina Hajiya da suke zargin tawagar wancan dan takara ya yi.

Shaidun gani da ido sun ce da kurar ta lafa, sai shi Injiniya Abba Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida) ya je don ya yi mata korafin abinda dogaranta su ka yi, a matsayin ta na kawar mai dakinsa, inda ta nuna matukar bacin ranta, har ta ke cewa ba za ta bari ya zama Gwamna a Kano ba.

Daga nan dai, in ji majiyoyi, sai ga karin jami’an tsaron farin kaya sun zo, inda su ka tsare Abba Gida-gida har sai da Aisha Bichi ta shiga jirgi ta tashi zuwa Abuja.

Wasu majiyoyin ma sun ce kafin ta tashi zuwa Abuja, a lokacin da ta ke ta fada, Aisha Bichi ta hango wani hadimin Abba Gida-gida, Garba Kilo yana daukar ta a waya, inda ta sa dogaran ta su “Harbe shi kuma ba abin da za a yi.” a cewar majiyar data nemi a sakaya sunanta.

Uwar Gidan babban Daraktan Hukumar tsaron farin kayan ta ci gaba da fada, ta kuma rantse cewa Abba Gida-gida ba zai shiga jirgi daya da ita ba. Haka dai aka ci gaba da tsare Abba har sai da jirgin ya tashi da matar Daraktan,” in ji majiyar.

Lamarin ya faru ranar Lahadin data gabata, amma kuma wata majiya da bamu tabbatar da sahihancinta ta rawaito cewa, Uwargidan Daraktan Hukumar tsaron farin kayan ta je har gida inda ta baiwa shi Abba Kabir Yusif hakuri bayan jan kunenta da maigidanta ya yi tare da umartarta take ta bashi hakuri.

Alhaji Abba Gwale shima ya yi tsokaci Kan wannan sabata juyetan da ke kara haska wani lamari da ke bukatar yi wa kallon tsanaki, inda ya bayyana cewa, Duk Nijeriya mutane 15 doka ta sahalewa yin amfani da jiniya (Amsa Kuwwa). A ciki babu shugaban jami’an tsaro na farin kaya ballantana matar sa, kuma hukuncin yin amfani da jiniya ga wanda doka bata amince masa ba.

A wani bangare kuma, Shugaban hukumar DSS Yusuf Magaji Bichi, ya bayyana cewa, ya bayyana cewa, ya gano wani shiri na musamman da wasu suka nyi don bata masa suna dana iyalansa, wannan kuma yana faruwa ne saboda mastayarsa ba kan wasu kururin gwamnati da kuma yadda yake gabatar da aikinsa ba tare da tsoro ba.

Ya ce wadannan mutane sun shirya amfani da kungiyoyi masu zaman kansu wajen shirya zanga-zanga da taruka inda za su yi kokarin bata masa suna dana iyalansa.

Yusuf Bichi ya na magana ne a takardar sanarwa da mai magana da yawujn hukumar DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Abuja.

Ya kuma tabbatar da faruwar takaddama a tsakanin matar Yusuf Bichi da dan takarar gwamnan Jihar kano na jami’iyyar NNPP a filin jigin saman a Malam Aminu Kano inda jami’an DSS da ke rakiyar Aisha Bich suka dakatar da Abba Gida-gida shiga jirgin saman, suna mayar da martani ne bayan da motocin da ke cikin tawagar Abba Gida-gida suka tare hanya abin da ya jawo wa Aisha Bichi jinkiri ita da jama’ar ta.

Sanarwa ta kara da cewa, “Hukumar DSS ba za ta zura ido tana kallon wasu gungun jama’a suna furucin raini ga shugaban da ma’aiakatan hukumar ba saboda wata mastalar da suke fuskanta, kuna kuma kira ga al’umma da su yi watsi da duk wata farfaganda na batanci da za a yi na bata sunan shugaban hukumar.

“Muna kuma kara jaddada goyon bayanmu ga shugaban kasa za kuma mu ci gaba da fuskantar duk wata barazana da ke nemi kawo cikas ga zaman lafiyar kasar nan musamman zaben da ke tafe a cikin wannan shekarar.” In ji sanarwar