Masarautar Katsina ta kori basaraken da yake hada baki da ‘yan ta’adda

0
97

Masarautar Katsina da ke Najeriya ta tabbatar da korar wani babban basarake, wato Makaman Sulefor bisa zargin sa da tallafa wa ayyukan ta’addanci a gundumarsa.

Jaridar Premium Times ta ce, ta ci karo da wata takardar wasika da aka rubuta ta a ranar 19 ga wannan wata na Janairu wadda ta bayyana cewa, Kauran Katsina wanda shi ne Hakimin Rimi, Aminu Nuhu, an kore shi daga kujerarsa bayan wani kwamitin da  gwamnati ta kafa ya same shi da aikata laifukan da mutanensa ke zargin sa da aikatawa.

Mai magana da yawun Masarautar Katsina, Ibrahim Bindawa, ya tabbatar wa Premiun Times da matakin tube rawanin basaraken.

Ba a karon farko kenan ba da ake sauke sarakuna a yankin arewa maso yammacin Najeriya sakamakon zargin su da goyo wa ‘yan ta’adda baya.

‘Yan ta’adda da ke kaddamar da hare-hare ba-ji-ba-gani sun kashe mutane da dama a jihohin arewa maso yammacin Najeriya musamman a Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna tare da raba miliyoyi da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here