Wasu da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne sun raba wa jama’a makudan kudade a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno na jihar Borno a yankin Tafkin Chadi, rabon kudin da ke zuwa bayan babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita wa’adin ci gaba da amfani da tsaffin kudade zuwa ranar 10 ga watan Fabarairu.
Wasu ganau sun bayyana yadda mayakan suka tsaya akan titi dauke da buhunhunan tsaffin kudin da suka kunshi Naira 200 da 500 da kuma 1000 suna rarrabawa matafiyan da ke bulaguro akan hanyar.
Shaidun gani da Ido sun bayyanawa Jaridar Daily Trust a Najeriyar yadda mayakan na ISWAP suka yi shigar kayan sarki tamkar Sojoji tare da girke motocin sulke guda 2 akan hanyar inda suke tare motocin suna bin fasinjojin daya bayan daya da kyautar tsaffin kudin a babbar hanyar da ke karamar hukumar Guzamala.
Wani da ke cikin fasinjan da suka samu wannan tagomomashi ya shaidawa manema labarai cewa mayakan na ISWAP sun baiwa kowanne fasinja da ke cikin motar kudin da yawansu ya kai dubu 100.
Wani fasinjan na daban ya bayyana cewa mayakan sun rika damkawa jama’a kudaden a hannunsu tare da fadin ‘‘kuje bankuna ku sauya su da sabbin kudade, Allah ya sa su zama masu amfani a gare ku’’.
Wannan dai ne karon farko da ake ganin irin wannan lamari a Najeriyar dai dai lokacin da jama’a ke fama da matsin rayuwa da kuma hauhawar farashin kayaki.
A lahadin da ta gabata ne dai babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita lokacin amfani da tsaffin kudaden don baiwa jama’a damar kammala sauya takardun kudin da ke hannunsu.