{"id":13363,"date":"2023-05-02T10:42:23","date_gmt":"2023-05-02T09:42:23","guid":{"rendered":"https:\/\/dailynews24.ng\/hausa\/?p=13363"},"modified":"2023-05-02T10:42:23","modified_gmt":"2023-05-02T09:42:23","slug":"dalibin-islamiyya-ya-gina-gadar-naira-miliyan-12-8-a-ogun","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dailynews24.ng\/hausa\/2023\/05\/02\/dalibin-islamiyya-ya-gina-gadar-naira-miliyan-12-8-a-ogun\/","title":{"rendered":"Dalibin islamiyya ya gina gadar Naira miliyan 12.8 a Ogun"},"content":{"rendered":"

Dosumu Kazeem, dalibin makarantar Madrasatul Da\u2019Watul Haqq, Leme, Abeokuta, ya bayar da gudummawar gina gadar da kudinta ya kai miliyan 12.8 ga al\u2019ummar Itesiwaju da ke Idi-Aba, Oke-Odo, yankin Olokuta a Abeokuta, Jihar Ogun.<\/a><\/p>\n

Gadar dai ta hada al\u2019umma zuwa karshen Olokuta na Idi-Aba, a karamar hukumar Abeokuta ta Kudu.<\/p>\n

An tattaro cewa gadar ita ce hanya daya tilo ga daliban makarantar Baptist Girls College, Abeokuta Grammar School da sauransu.<\/p>\n

Mai bayar da tallafin mai shekaru 40, wanda kuma manomi ne, ya ce ya gudanar da aikin ne tallafin daga iyayensa domin rage radadin da yaran makaranta da sauran al\u2019umma ke ciki.<\/p>\n

Wannan aiki, kamar yadda ya bayyana, an ba shi fifiko ne a cikin kudin aikin gidansa na kashin kansa, kamar yadda ya fasa yin aikin Umrah zuwa Saudiyya don ba shi damar kammala gadar.<\/p>\n

\n