{"id":19073,"date":"2024-03-27T10:33:09","date_gmt":"2024-03-27T09:33:09","guid":{"rendered":"https:\/\/dailynews24.ng\/hausa\/?p=19073"},"modified":"2024-03-27T10:33:18","modified_gmt":"2024-03-27T09:33:18","slug":"yan-bindiga-basu-da-banbanci-da-yan-taadda-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dailynews24.ng\/hausa\/2024\/03\/27\/yan-bindiga-basu-da-banbanci-da-yan-taadda-tinubu\/","title":{"rendered":"Yan bindiga basu da banbanci da yan ta\u2019adda – Tinubu"},"content":{"rendered":"\n
Shugaba Bola Tinubu<\/a> na Najeriya ya bayyana cewa ya zama dole a ri\u0199a \u0257aukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin \u01b4an ta\u2019adda.<\/p>\n\n\n\n Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron bu\u0257e-baki tare da ma\u2019aikatan shari\u2019a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin al\u0199alin al\u0199alai na \u0199asa, mai shari\u2019a Olukayode Ariwoola.<\/p>\n\n\n\n Da yake nanata \u0199udirin gwamnati na mur\u0199ushe \u01b4an bindiga, shugaba Tinubu ya ce wa\u0257anda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.<\/p>\n\n\n\n \u201cDole ne mu ayyana masu garkuwa a matsayin \u01b4an ta\u2019adda,\u201d in ji shugaban \u0199asar, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ta ruwaito.<\/p>\n\n\n\n Najeriya dai tana fama da \u0199aruwar matsalolin tsaro. Yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas sun yi fama da \u0199aruwar sace-sacen mutane da hare-haren \u01b4an bindiga a shekaru 10 da suka gabata.<\/p>\n\n\n\n Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa ba za ta tattauna da \u01b4an bindiga ba duk da yadda suka mayar da sace mutane don ku\u0257in fansa a matsayin wata hanyar samun ku\u0257i inda suke garkuwa da \u0257alibai da jama\u2019a \u2013 hari na baya-bayan nan shi ne sace \u0257alibai 137 daga Kuriga a jihar Kaduna<\/a>.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":" Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana cewa ya zama dole a ri\u0199a \u0257aukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin \u01b4an ta\u2019adda. Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron bu\u0257e-baki tare da ma\u2019aikatan shari\u2019a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin al\u0199alin al\u0199alai na \u0199asa, mai shari\u2019a Olukayode Ariwoola. Da […]<\/p>\n","protected":false},"author":12,"featured_media":18658,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[18],"tags":[609,2149],"yoast_head":"\n