Shugabannin ASUU sun ki amincewa jama’a su yi karo-karon kudade domin biya wa kungiyar bukatun da suka sa ta shiga yajin aiki ne bayan an yi musu tayin hakan a safiyar ranar Asabar.
Gabanin haka, mai gabatar da shiriye shirye a wani gidan Radio a Abuja Ahmed Isah, ya kafa asusun tara wa kungiyar kudade domin share mata hawaye ta janye yajin aiki.
Akwai bukatar alummar Kano su tallafawa ilimin mata – Ajiyan Gaya
A yau asabar Ahmed Isah, ya gabatar da Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel, ya bayar domin sanyawa a asusun tallafin da aka bude a bankin TAJ.
Sai dai shugaban kungiyar ya nesanta kungiyar da kudaden da ake tarawa.