Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin Firimiyar Ingila na bana bayan doke Aston Villa daci 3 – 2 a wasan karshe da suka doka dazu.
Dafari dai Aston Villa ce ta sha gaban City da kwallaye 2 amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Manchester City ta zura kwallaye 3, kuma aka tashi wasa haka.
Manchester City ta lashe kofin ne da maki 93 kuma wannan shi ne karo na 8 da ta ke daukar sa a tarihin ta.
A gefe guda kuma Liverpool ta doke Wolves da ci 2 – 1 wanda hakan ya sa ta karkare gasar a mataki na biyu da maki 90.
Sauran wasannin da aka doka Arsenal ta casa Everton da ci 5 – 1, Tottenham 5 – 0 Norwich City, Crystal Palace 1 – 0 Manchester United.
A yanzu dai Manchester City da Liverpool da Tottenham dakuma Chelsea su ne zasu wakilci Ingila a gasar Cin kofin zakarun turai na Champions League a badi bayan sun karkare a matakin ‘yan hudu a teburin Firimiyar.