Hukumar yaki da safarar bil’adama ta kasa NAPTIP ta ceto wasu mutum goma da aka yi fataucinsu a Jihar Kano.
An ceto mutanen ne da ke kan hanyar zuwa Jamhuriyyar Nijar domin yin aikatau.
Babban jami’in NAPTIP a shiyyar Arewa maso Yamma, Barista Abdullahi Babale, ya ce an ceto mutanen ne wadanda aka yi fataucinsu daga Jihohin Kogi, Delta, Kwara, Oyo, Ondo, Legas, Ogun da kuma Osun.
Kungiyar ASUU ta yi watsi da tayin kudaden da akai mata domin ta janye yajin aiki
Babale ya ce hukumar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ke kula da shige-da-fice a kan iyaka, sun ceto mutanen wadanda suka kunshi maza biyu da mata takwas ’yan tsakanin shekaru 9 zuwa 28.
Ya ce, a halin yanzu ana ci gaba da ba su shawarwari a wani matsuguni da hukumar ta tanada, yayin da ake kokarin mika su ga ’yan uwansu.