Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta nada Mr José Santos Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.
Nadin ya soma aiki ne nan ta ke.
José Vitor dos Santos Peseiro, mai shekaru 62, dan kasar Portugal na zama fitaccen Dan wasan gaba lokacin dayake buga tamola.
Gwamnatin tarayya zata amince da filin wasan jihar Sokoto domin buga wasannin kasa da kasa
Haka kuma ya taba horas da kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar tura da Asia da Africa dakuma kudancin Amurka.
Zalika ya yi karatu inda ya samu digirin sa na farko a fannin wasanni.
Ana saran Peseiro ya jagorancin Super Eagles a wasannin sada zumuncin da za ta yi da kasashen Mexico dakuma Ecuador a ranekun 28 ga watan Mayun da muke ciki dakuma 2 ga watan Juni.
NFF ta kuma nada tsohon dan wasannan Finidi George a matsayin mataimakin Peseiro na daya da Salisu Yusuf na biyu.