Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes sun farwa ‘yan wasa da jami’an kungiyar Lobi Stars.
Lamarin ya faru ne yayin wasan mako na 30 na gasar firimiyar Najeriya da kungiyoyin biyu suka fafata a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna.
Tinubu ya taya Atiku Abubakar murnar zama dan takarar Shugaban kasa
Dama dai an haramtawa Niger Tornadoes buga wasa a Minna inda aka meda ita zuwa Kaduna saboda matsalar tsaro.
Lamarin ya fara ne bayan bangarorin biyu sun tashi babu ci a kashin farko na wasan.
Jim kadan bayan dawo war ‘yan wasa domin cigaba da fafatawa sai wasu bata gari da ake zargin magoya bayan Niger Tornadoes ne suka afkawa jami’ai da ‘yan wasan Lobi stars.
Rahotanni sun ce sun ji musu ciwo sosai tahanyar yin amfani da wukake dakuma fasassun kwalabe.
Haka kuma sun lakadawa alkalin wasa duka lamarin da ya kai ga tashi daga wasan kwata-kwata.
Jami’an tsaron dake bada tsaro a wasan sun kasa yin komai lokacin da lamarin ke faruwa.