Lauyoyi tara sun kai Safara’u da Gwanja da Murja ƙara Kotun Musulunci

0
123

Wasu lauyoyi guda tara sun kai wasu mutum goma ƙara waɗanda suka shahara a shafin Tiktok.

Mai magana da yawun Kotunan Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC da lamarin inda ya ce lauyoyin sun rubuta takardar koken inda suka ce mutane goman na ƙoƙarin ɓata tarbiyya ta hanyar yin waƙoƙin batsa da baɗala.

Lauyoyin sun shigar da ƙarar ne a gaban Kotun Daukaka Ƙara ta Shari’ar Musulunci da take Bichi inda daga baya kotun ta buƙaci kwamishinan ƴan sanda na jihar da a lalubo mutanen a gudanar da bincike a kansu.

Cikin mutanen da suka sharara a tiktok da aka kai ƙararsu akwai Mista 442 da Safara’u da Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Saraki.