Jiragen sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP a tafkin Chadi

0
100

Jiragen yakin sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin ISWAP uku a maboyar kungiyar a yankin Tafkin Chadi.

Wata majiyar tsaron ta tabbatar da mutuwar manyan kwamandojin kungiyar uku a harin, da suka hada da Mohammed Balke, Malam Ciroma da Bashir Sniper.

Mutanen uku sun mutu ne a lokacin da jirgin ya jefa bam a maboyarsu da ke Jibilaram.

Mohammed Balke shi ne shugaban gidan yari kuma mai kula da masu garkuwa da mutane na ISWAP; Malam Ciroma shi ne mataimakinsa na biyu; Bashir Sniper kuma shi ne kwamandan kungiyar da ke kula da hanyoyin shiga dukkan tsibiran da ke karkashinta.

Wata majiyar tsaro ta ce a ranar Talatar jiragen yakin sojin Najeriya suka yi luguden bama-bamai a tsibiran Jibillaram da Rino da Kangarwa, wadanda sansanoni ne na kungiyar ISWAP inda suka kashe mayakan da dama tare da yi wa kungiyar ta’addancin mummunar barna.