Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya ziyarci Kano a domin yin ta’aziya ga Sanata Kabiru Gaya kan rasuwar dansa.
Osibanjo ya bayyana rashin Sadik Gaya a matsayin rashi baga iyalansa ba.
Ya bukaci iyalai da yan’uwan da yin hakuri tare da cigaba da yi musu addua.
Wakilyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Farfesa Yemi Osibanjo ya samu rakiyar gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje zuwa gidan Kabiru Gaya.