Gwamnatin Tunisia ta ƙara farashin fetur da gas ɗin girki

0
90

Gwamnatin Tunisia ta ƙara farashin man fetur da kashi uku cikin 100 inda farashin tukunyar iskar gas ta ɗaga da kashi 14 cikin 100.

Matakin wani yunƙuri ne na rage tallafin makamashi domin cika wata muhimmiyar buƙatar asusun lamuni na duniya IMF.

Tunisia na neman bashin dala biliyan uku domin taimaka mata magance yanayin da jama’a ke ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin kayan masarufi da ba za ta iya ci gaba da shigowa da su daga ƙasashen waje ba.

IMF da sauran hukumomin lamuni na ƙasashen waje na neman a rage tallafi da yi wa kamfanonin gwamnati garambawul.