Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya samu karuwa

0
91

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sadarwa, Bashir Ahmad ya samu karuwa tare da matarsa kamar yadda ya bayyana shafinsa na Twitter.

Ahmad Bashir ya auri matarsa ne a watan Satumba na shekarar 2020 a jihar Kaduna, inda suka samu karuwa karo na farko a yanzu.

A kwanakin baya sunan Bashir Ahmad ya mamaye gidajen labarai bayan ya ajiye aikinsa na hadimin shugaban kasar ya nemi dan majalissa a jihar Kano.

Amma ya fadi zaben fidda inda yace magudi aka yi masa, kafin daga bisani ya koma wurin shugaba Buhari ya sake bashi wannan mukamin na hadiminsa.