Gwamnatin Kano ta yi martani kan matsalar gurbataccen ruwan sha da ake samu 

0
97

Gwamnatin jihar Kano ta ce, tana dab da shawo kan matsalar gurbataccen ruwan sha da ake samu a baya-bayan nan.

Kwamishinan ma’ikatar samar da ruwan sha Alhaji Garba Yusuf Abubakar ne ya bayyana hakan a yau a Kano.

Alhaji Garba Yusuf ya kuma ce, matsalar gurbacewar ruwan ta faru ne sakamakon fashewar bubutun tunkudo ruwan da suke Tamburawa.