Ba za mu bari ɗalibai su rufe hanyar Kaduna-Abuja ba – Gwamnati

0
127

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za ta yarda da duk wani yunkuri da wani ko wasu za su yi na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga ba.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ne ya yi wannan gargaɗin a wata sanarwar da ya fitar a yau Talata a Kaduna.

Ya ce gwamnatin ba za ta amince da zanga-zangar ba domin hakan ka iya haifar da karya doka da oda.

“Wannan sanarwar na gargaɗi cewa kada a yi wani yunkuri da zai tauye wa ƴan ƙasa hakkinsu na tafiye-tafiye domin samun zaman lafiya.

“Duk da cewa gwamnatin Kaduna ba ta tauye wa mutane hakkinsu na nuna rashin amincewarsu a kan wani abu, amma ba za kuma batun tsaro kullum shine a gaba a wajenta,” in ji sanarwar.